WANI MATASHI YA BUDEWA MOTAR SARAUNIYAR INGILA WUTA

0

A kudancin kasar New Zealand wani matashi ya kai wa Sarauniyar Ingila hari ta hanyar bude wa motar ta wuta, a lokacin da ta kai wata ziyara birnin Dunedin dake tsibirin kudancin kasar New Zealand.
A bayanin wasu takardun sirri na hukumar leken asirin New Zealand, saurayin mai suna Christopher Lewis bai samu nasarar jiwa kowa ciwo ba.
An kama saurayin mai shekaru 17 da haihuwa zuwa gidan horo da zargin fashi da makami, inda aka ba da rahoton cewa yana da tabin hankali.
Sai dai ‘yan jarida da yawa basu yadda da bayanan ba, inda suka shiga neman ainihin yanda lamarin ya faru, sun gano cewar akwai lauje cikin nadi, saboda akwai alamun ‘yan sanda sunyi shaidar zur ne.
A baya bayan nan, an fitar da rahotanni daga wurin jami’an leken asirin kasar, inda suka nuna cewa, an rufe gaskiyar abinda ya faru dinne domin gudun kada Sarauniyar ta sake cin karo da irin wanan barazanar a lokacin da zata kai wata ziyarar kasar. Sannan kuma an tabbatar da cewa yaron kalau yake bai da tabin hankalin komai.
Sai dai ba a samu damar yankewa Lewis hukunci ba dalilin kashe kanshi da yayi a gidan wakafi, wanda hakan shine yayi dai dai da hukuncin yunkurin kashe sarauniyar Ingila da yayi.

KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.