Tsohuwa ta kashe danta don gudun zuwa gidan tsofaffi

0

Ana tuhumar Anna Mae Blessing da kisa da sace mutum

‘Yan sanda a Amurka sun ce wata tsohuwa mai shekara 92 ta kashe danta mai shekara 72 da bindiga domin ta hana shi kai ta gidan kula da tsofaffi.
Anna Mae Blessing, wadda ake tuhuma da kisan gilla ta nuna rashin jin dadinta game da aniyar danta na kai ta gidan kula da tsofaffi, kamar yadda takardun da aka gabatar a gaban kotu suka bayyana.
“Ka raba ni da raina, a kan haka zan dauki naka,” haka rahotanni suka ruwaito tsohuwar na cewa lokacin da ‘yan sanda suka zo gidan da take zaune da danta da buduwarsa a Arizona.
Misis Blessing ta fada wa ‘yan sanda cewa ta so ta kashe kanta.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar 2 ga watan Yuli a garin Fountain Hills, da ke karamar hukumar Maricopa, in ji kafofin watsa labarai na garin.
Dan Misis Blessing, wanda ba a bayanna sunansa ba ya so ta koma gidan kula da tsofaffi saboda babu “jituwa” tsakaninsu.
‘Yan sanda sun ce mahaifyar mutumin ta boye bindigogi biyu a cikin rigarta kafin ta tunkari danta a cikin dakinsa
A lokacin da gardama ta kaure tsakaninsu, ta fitar da daya daga cikin bindigogin da ke hannunta, wadda ta saya a shekarar 1970 kuma ta harbe shi.
‘Yan sanda sun samu dan a mace, kuma akwai raunukan harbin bindiga a wuyansa da makogoronsa.
Misis Blessing ta kuma nuna wa buduwar danta mai shekara 57 bindiga, wadda ta kwace bindigar daga hannunta ta jefar a wani bangare na dakin.
Sai kuma ta fitar da bindiga ta biyu, wadda ta fada wa ‘yan sanda cewa mijinta da ya rasu ne ya ba ta a shekarar 1970.
Sai dai budurwar ta kabe bindigar daga hannun Misis Blessing kafin ta tsere kuma ta kira ofishin ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun gano Misis Blessing kan wata kujera da ke dakinta. Daga bisani ta fada mu su cewa ya kamata “a sata ta yi barci” saboda abin da ta yi.
Ana zarginta da kisan gilla da sace mutum, kuma za ta biya dala 500,000 a matsayin beli
Source From BBC Hausa
KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.