SUBEB TA HANA WAZIFA A TSANGAYAR MAKARANTUN BAUCHI

0

Rahotanni sun kawo cewa hukumar kula da ilimin bai daya wato SUBEB sashin jihar Bauchi ta bukaci makarantun Tsangaya da su daina yin wazifa ko karanta salatul fatihi a hidimar makarantar.
A cewar hukumar hakan baya daga cikin tsarun makarantun a fadin jihar da ma tsarin hukumar UBEC ta fitar akan karatun Tsangaya.
Wannan bayani na tattare ne a wata takarda da shugaban hukumar ta SUBEB Yahaya Ibrahim Yaro ya fitar da sanya hannun sakataren hukumar Mahmeed A. Kari.
An saki wasikar ne a ranar 5 ga watan Fabairu mai taken wasikar dakatar da wazifa da salatil fatihi mai addireshi kai tsaye zuwa ga Shugabannin makarantun Tsangaya-Tsanya da suke fadin Bauchi.
Hukumar ta yi bayanin cewar ta samu korafin cewar ana tilasta wa dalibai yin wazifa da salatil fatihi.
Jaridar Leadershin ta rahoto cewa wannan mataki bai yi wa mamallakin wannan makarantar Tsangayar Sheikh Dahiru Bauchi dadi ba.

KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.