Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda

0

Manyan sojojin Najeriya sun yi kira da gwamnatin tarayya ta kara wa rundunar ‘yasanda Najeriya ma’aikata
– Sojojin Najeriya sun ce aikin warware matsalolin cikin gida na ‘yansanda ne ba na sojoji ba
Rundunar sojin Najeriya ta ce, cigaba da sa su yin aikin ‘yansanda a kusan jihohi 32 a fadin kasar, yana ci musu tuwo a kwarya.
A lokacin da aka gudanar da taron manyan jami’an sojojin karo na 40 a Kwalejin Sojoji dake Jaji a jihar Kaduna, manyan jami’an sojojin Najeriya sun yi kira da gwamnatin tarayya ta kara wa rundunar ‘yasandan Najeriya ma’aikata.
Sojoji sun ce kara wa rundunar yansadar Najeriya ma’aikata da yi musu horon da zai sa su iya aikin su kamar yadda yakamata ya zama dole.
Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda
Sun ce ba dai-dai bane a ce kasa kamar Najeriya mai yawan mutane sama da miliyan 182 ta na da jami’an ‘yansanda kasa da 40,000

Sojojin sun ce aikin su shine kare iyakokin kasar, ba wai war-ware riginginmu cikin gida ba wanda shine aikin ‘yasanda a kasashen da suka cigaba.

KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.