Mai maganin bindiga ya mutu wajen gwajin ta

0

Maganin bindiga  ne mai farin jini a Najeriya duk da rahotannin wadanda suka mutu wajen gwada ingancinsa

Wani mai maganin gargajiya a Najeriya ya mutu bayan da daya daga cikin abokan cinikinsa ya gwada karfin “maganin bindigan” a kansa.
Mai maganin, Chinaka Adoezuwe, mai shekara 26 da haihuwa ya mutu bayan da ya umarci mutumin da ya harbe shi da bindigar a yayin da yake sanye da wasu layu a wuyansa.
‘Yan sanda a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar sun ce an kama mutumin da yayi harbin kuma ana tuhumarsa da aikata kisan kai.
Maganin bindiga da danginsa kamar maganin wuka na da farin jini sosai a Najeriya, kuma mutane da dama kan nemi masu maganin gargajiya da su taimakesu da magungunan.
Amma an sha samun rahotannin wadanda suka mutu bayan gwajin maganin bindiga a kasar.
KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.