Kalli Yanda Sojojin Najeriya ‘sun yi wa Boko Haram luguden wuta a Dajin Timbuktu’

0 277

Dakarun sojin Najeriya ƙarƙashin Shirin Lafiya Dole mai yaƙi da Boko Haram sun yi luguden wuta a Timbuktu, wani ɓangare mai sarƙaƙiya a dajin Sambisa da yankunan kusa da Tafkin Chadi.

Rahotanni sun ce sojoji sun kwashe tsawon mako guda suna ɗauki-ba-daɗin fatattakar ‘yan ta-da-ƙayar-baya a yankin, abin da kuma ya yi sanadin mutuwar gomman ‘yan Boko Haram.

Bayanai sun ce Dajin Timbuktu, wanda ya ratsa tsakanin jihohin Borno da Yobe, ya yi ƙaurin suna don kuwa a tsawon shekara huɗu da suka gabata, sojoji sun gaza shigarsa ta ƙasa.

Sai dai a yanzu ga dukkan alamu ta faru ta kare, ƙoƙarin haɗin gwiwar sojojin Sashe Na Biyu da kuma dakaru na musamman daga sojin ƙasa na Najeriya, da haɗin gwiwar sojojin sama da ayyukan sa ido a kan kai-komon abokan gaba, ya wanzar da kyakkyawan sakamako.

Bayanai sun ce aikin fatattakar wanda ke ci gaba da gudana ya yi sanadin ‘yantar da Buk da Talala da Gorgi waɗanda dukansu tungar ‘yan Boko Haram ne da ke da ƙarfi.

Jaridar PRNigeria ta ce samamen ya sa ala dole, ba girma ba arziki kwamandojin Boko Haram, irin su Ameer Modu Borzogo da Modu Sullum sun tsere daga yankin.

Wata majiya mai ƙarfi da BBC ta tuntuba da ba ta amince a bayyanata ba, ta ƙara tabbatar da batun kai waɗannan hare-hare da suka sa ƴan ƙungiyar ta Boko Haram ranta cikin na kare a dajin, wanda suke ganin ya zama mallakinsu shekara da shekaru.

“Tabbas babu shakka dakarun Najeriya sun shiga wannan daji na Timbuktu,” a cewar wannan kafa, “kuma bayan wannan daji za su doshi yankunan da ke iyaka da tafkin Chadi domin su yi shara da kakkaɓe duk ‘yan wannan ƙungiya da su ka yi saura.”

Haka zalika, sojoji sun yi nasarar kuɓutar da mata da ƙananan yara da mayaƙan Boko Haram suka sace.

Yaya masana ke kallon lamarin?

Barista Bulama Bukarti mai bincike kan al’amuran tsaro a Afirka ya ce idan har wannan labari ya zama tabbas to lallai abin a jinjinawa sojojin Najeriya ne, domin dajin Timbuktu wani ƙasurgumin waje ne a cikin dajin Sambisa.

“Wasu rahotanni ma na cewa shi kansa Abubakar Shekau shugaban ƙungiyar Boko Haram a can yake a ɓoye, sannan an shafe sjehekaru sojojin Najeriya na samun wahalar shiga cikin dajin, saboda dalilai da dama,” in ji Bukarti.

Dalilan da suka sa shiga Dajin Timbuktu ya dinga yi wa sojoji wahala a baya

Na farko shi ne nisansa, sabooda yana can cikin dajin Sambisa.

Abu na biyu kuma ƴan Boko Haram sun kewaye hanyar shiga dajin da bama-bamai, irin waɗanda ake binne su a cikin ƙasa wato landmine, ta yadda idan sojoji suka yi ƙoƙarin shiga sai bama-bamai su yi ta tashi da su.

Na uku kuma hanyar wajen akwai taɓo sosai ta yadda idan sojoji suka yi ƙƙarin shiga da kotocinsu sai taɓo ya yi ta riƙe su ta yadda ba za su iya shiga ba. Kenan yanzu idan yanzu har suka samu dabarar shiga dajin, to lallai sun yi ƙoƙari.

Masu sharhi sun yaba wa wannan ƙoƙari na sojojin NAjeriyar

Barista Bukarti ya ƙara da cewa: “Amma fa wannan nasara za ta zama ta daban ce idan har ta ƙasa sojojin suka shiga ba ta sama ba. Don idan ta sama ne to ba sabon abu ba ne, do ko a bara ma rundunar sojin ta kai hare-hare Dajin Timbuktun ta sama.

“Kuma yanzu mun san cewa ƴan Boko Haram sun koyi dabarun zillewa hare-haren sama a shekarun da suka kwasa suna yaƙi, kuma ba a cika samun nasara a hare-haren sama ba. Don haka in dai har sun shiga ta ƙasa to lallai sun isa a jinjina wa sojojin Najeriya.

Wani ci gaba da aka samu shi ne yawacin hare-haren da ayyukan da sojojin haɗin gwiwar na Najeriya, suka yi shi ne ragargaza da wasu tungayen ‘yan ƙungiyar ta Boko Haram a Kidari da Argude da Takwala da Chawalta Da Galdekore, wannan kuma duk da tsayuwar daka da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi.

Yanayin tabbas da rashin nasara da ya mamaye ‘yan kungiyar ta Boko Haram, ya saka su yin amfani da bama-bamai masu aman wuta irin na masu kai harin kunar bakin wake kan sojojin, abin da ya sa suka raunata wasu sojojin wasu kuma ƴan ƙalilan suka rasa rayuka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.