Ina shawara kan makomata a APC – Tambuwal

0

Gwamna Tambuwal ya halarci wani taron da BBC ta shirya a birnin Legas a kudancin Najeriya


Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce yana nazari kan ficewa jam’iyyar APC da kuma yiyuwar komawa jam’iyyar PDP.
Tsohon shugaban majalisar wakilan kasar yana cikin mambobin jam’iyyar APC da ake kira ‘yan sabuwar PDP da ke takun-saka da gwamnatin Shugaba Buhari.
Gwamna Tambuwal ya shaida wa BBC cewa yana nan yana nazari tare da jama’arsa game da ko zai ci gaba da zama a jam’iyyar APC ko kuma akasin haka.
Gwamnan kuma bai musanta yiyuwar sake koma wa jam’iyyar PDP da ke adawa ba, bayan an tambaye shi ko PDP zai koma kamar yadda ake rade-radi.
“Ba a yin siyasa a boye, duk abin da muka tanada muka yi shawara a kan shi, ba da dade wa za mu fito da shi,” in ji Gwamna Tambuwal.
Daga nan ya ce bayan sun kammala cimma matsaya zai fito ya fada wa duniya.
Gwamnan na Sakkwato ya fadi hakan ne a wani taron da BBC ta shirya a birnin Legas a kudancin Najeriya.

Kalamansa na zuwa bayan daya daga cikin ‘yan sabuwar PDP tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanatan APC Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yanzu shi ba dan kowace jam’iyya ba ne.
Kwankwaso kuma ya yi ikirarin zai iya doke Shugaba Buhari idan jam’iyyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.
Tsohon gwamnan na Kano wanda bai fito karara ya bayyana aniyar neman kujerar shugaban kasa ba, ya ce: “yanzu a shirye yake ya gwada sa’arsa wasu wurare kuma ya san cewa PDP babbar jam’iyya ce da ke da karfin kayar da Buhari.”
APC ta fada cikin rigingimu tun bayan da ta lashe zaben shekarar 2015, lamarin da ya kai ga wasu ‘ya’yanta ficewa daga jam’iyyar baki daya, yayin da a yanzu wasu manyan jiga-jiganta ke barazanar ficewa.
A ranar Laraba ne wasu tsoffin ‘yan sabuwar PDP suka sanar da kirkiro wani bangare a jam’iyyar APC, da sunan Reformed APC, ko rAPC tare da bayyana Injiniya Buba Galadima a matsayin shugabansu.
Amma a sanarwar da ta fitar uwar jam’iyyar ta APC ta musanta ikirarin na sabon bangaren, tana mai cewa ba ta san da wani bangaranci ba kuma wadanda suka sanar da kafa bangaren har yanzu ‘ya’yanta ne.
Rikicin bangarori a APC da kuma barazanar ficewa daga bangaren ‘yan sabuwar PDP ya dada fito da girman kalubalen da ke gaban jam’iyyar kafin zaben 2019.
A watan Fabrairu ne Shugaba Buhari ya nada Bola Tinubu a matsayin jagoran dinke barakar da jam’iyyar APC ke fuskanta a fadin kasar.
Amma har zuwa yanzu babu wani sasanci da aka kulla ko aka gani tsakanin bangarorin da ke rikici a jihohin na APC.
KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.