Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin gina gidajen da aka lalata a Kudancin Kaduna

0

Hukumar SEMA ta yi alkawarin taimakawa kwamitin sulhu da Osinabjo yake jagoranta
Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sake gina gidajen da aka lalata a lokacin da rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kudancin jihar Kaduna.
Kwamitin yin sulhu tsakanin manoma da makiyaya da mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbajo, yake jagoranta ta bayyana haka bayan sun kammala binciken su.

Wani jami’in gwamnatin tarayya mai suna, Mista James Akujobi, ya fadawa manema labaru cewa gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin gyara gidajen da aka lalata Kudancin Kaduna saboda ta na son mutanen yankin su, su cigaba da rayuwar su kamar yadda suka saba a da musamman manoma.
Sakataren hukumar ba da agaji na gaggawa na jihar Kaduna (SEMA), Mista Ben Kure, yace a matsayin su na masu karban baki za su taimakawa kwamitin sulhu da duk wani abun da take bukata.

KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.