‘Adan ina son ka, don Allah ka ajiye wukar ‘ – Inji wata bazawara a lokacin da tsohon Mijinta ya caccaka mata wuka

0

Wata mata mai suna Asiyah Harris ta gamu da ajalinta a hannu tsohon mijinta, Dahir Adan, bayan hafa masa yaya guda biyu kafin auren nasu ya mutu, inji rahoton jaridar Daily Mail.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar 22 ga watan Agustan shekarar da ta gabata a garin Bristol na kasar Amurka, inda Adan ya kutsa kai gidan Asiyah ya caccaka mata wuka a wuya har sau uku, daga nan tace ga garinku nan.

Shaidun gani da ido sun bayyana ma wata Kotu dake sauraron shari’ar cewar da kunnuwansu sun ji lokacin da marigayiyar ke kuka tana cewa “Adan don Allah ka yar da wukar, ina matukar kaunarka.” a lokacin da yake caka mata wukar, amma sai da ya kashe ta hankalinsa ya kwanta.
Asiyah
Shaidun, wadanda makwabtan Asiyah sun bayyana cewa a daren 21 ga watan Agusta, sun ji Asiyah da Adan suna daga murya suna cacar baki, hakan ya sa suka kira musu Yansanda. Sai washegari ma suka ji irin wannan rigimar a gidan, samma da zuwan Yansanda, sai suka tarar da gawar Asiyah jina jina.
Duk kokarin da masu bada agajin gaggawa suka yin a ganin sun ceto rayuwar Asiyah ya ci tura, saboda wukar da Adan ya caccaka mata ya yanka jijiyoyin wuyanta, ma’ana, abin gama ya gama. Sai dai majiyar ta ruwaito yayan nasu basa gidan a lokacin da lamarin ya faru.
Da yake yanke masa hukunci, Alkalin Kotun Peter Balic QC yace “Na tabbatar da kai ne ka kashe Asiyah, a yau na yanke maka hukuncin zaman gidan yari na dindindin.” Da fatan Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/KuryaLoaded
ko a http://twitter.com/KuryaLoaded
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar kanny24newsHausa cikin sauki

KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.