Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:9

0 0

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol

Ya ce, Ina cekiya min tun daga farko alhamdu zaki iya har zuwa sabbi. Ta ce,eh! Ai wata rana a gidan Abu na karamin ya ce to nima yau na kara miki tun daga fatiha suka fara tiryan-tiryan hara zuwa sabbi yai mamakin kokarin ta itama Amma mamaki taji. Ta ce, Ga yarinya da qoqari amma saboda mugunta an hanata karatu. Malam ya ce, Mu yiwa iyayenmu addua waxanda suka rasu Allah ya gafarta musu. Bayan sun gama ya ce, kullum in kika yi sallah ki ringa yiwa mahaifiyarki addua kin ji ko? Ta ce, To! Amma ta ce, Ni fa bangane muku ba naga alamar so ake akwacen miji. Ya ce, To ke ya kika g ani ai min yi daidaiko? Zulfau ta sunkuyar da kai cikin qafafunta. Ya ce, Uwargida tashi kiwo mana abin kari. Ta ce, To ya na iya tunda an mallaki min miji sai yanda Allah ya yi dani. Ta miqe ta xauko masa abin karin. Bayan ya gama ci ya yi wanka ya ce, Bari in fita kinsan yau ne sunan gidan malam Salmanu ta ce haka nima an aiko min. Suka yi masa addua Allah ya dawo dashi lafiya ya fice. Yau ma Zulfau bata koma gida sai dare a hankali yau ma ta lallava ta kwanta tana cikin barci taji saukar ruwa a jikinta kan ta farga an shiga dukanta ta koina ta shiga bata haquri. Ta ce, Haba yarinya ni za ki wulaqanta a gidan nan jiya wane irin nema ne ban miki ba gidan uban wa kika je? Cikin murya kuka ta ce, Wallahi ba inda naje ina gidan su amma sai dai ta yi mata lilis sannan ta kyale ta, ta yi ajiyar zuciya ta ce, Ko ubanki bai isa ya wulaqanta ni ba ballantana ke. Ta xauketa da mari. Ta ce, Kuma ki tashi ki xauki jarkoki ki xebo min ruwan don yau ba gidan uban da za ki. Haka ta miqe cikin tsamin jiki ta xauki jarka ta fice. Sai da tayo xauka goma sannan ta qyaleta ta xauki buta ta yi alwala ta yi sallah ta yiwa mahaifiyarta addua. Sannan ta tashi ta shiga xakin babanta ta gaishe shi bai amsa ba ya hau ta da faxa kamar ya daketa. Ya ce, Ina kike zuwa kwana biyu bana ganinki a cikin gidan? Ta ce, Abu ba nisa nake yi ba ina gidansu Amma ne. Ya ce, To me kike zuwa kina yi bayan kin san za ki yi mata aiki? Kar na kuma ganin kin je bana son ki vata mata rai. Ta ce, Ka yi haquri Abu in Allah ya yarda bazan sake ba. Ta tashi ta fice daga xakin cikin mamaki wai yau babanta ne yake ce mata ta daina vatawa Deeja rai, ko ya manta irin izayar da take yi mata ne hawaye suka shiga zubo mata tasa gefen xankwalinta ta share. Har ta kai bakin qofa zata fice daga gidan taji ta kwalama kira. Ke Zulfau gidan uban wa za ki kuma ce miki na yi kin gama min aiki da za ki fita? Sumui-sumui ta juyo ta dawo tana shirin zama. Ta ce, Ba zama na ce ki yi ba dashi za ki yi nasa ki wani aikin don ba kiga hutu a nan gidan ba. Maza tashi ki xauki wanke-wanke ki yi min gasu can. Ta miqe ta nufi inda kayansu ta fara wanke-wanke ji ta yi kamar ana kiran sunanta qasa-qasa ta juya Asabe ta gani a bakin qofa tana kiranta, ta tashi saxab-saxab ta tafi. Asabe ta ce, Zulfau me kike yi cikin wannan ranar mai zafi haka? Ta share zubar da ta tsantsabo mata ta ce, Wanke-wanke nake yiwa Deeja. A cikin ranar nan tun xazu ba a yi ba sai yanzu muje na taya ki. Zulfau ta yi saurin riqeta ta ce, Deeja tana nan fa a xakinta wallahi. To ina ruwana ke dai muje na tayaki. Ba yanda ta iya dole ta kyaleta. Tana wanke wa ita kuma tana yi mata xauraya har suka gama. Tattara kayan ta kai mata kicin ta ajiye Asabe ta ce, Zo mu tafi ki rakani. Ina kinsan fa kuma Babana ya hanani fita koina. Ta ce, Ba nisa yanzun nan zamu dawo ba daxewa zamu yi ba. To bari na gayawa Deeja kar ta fito babta ganni ba kinsan halinta. Asabe ta ce, Dalla kyaketa in kin dawo ta kasheki taga za a kyale ta ne. Zulfau ta ce, Ni dai tsoro nake ji. Ta finciki hannunta suka yi waje, suna tafiya suna hirarsu. Zulfau ta ce, Wai ke Asabe ina zamu je tun xazu sai faman tafiya muke ta yi? Ta yi murmushi ta ce, Wallahi Zulfau kin cika matsawa ai mun kusa kawowa. Wata gindin bishiya suka zauna. Zulfau ta ce, Wash! Wallahi duk na gaji yar tafiyar nan da muka yi. Asabe ta ce, Wallahi nima haka ta ce, Zulfau kin san wani abu, ta girgiza kai ta ce, Sai kin faxa. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, Zulfau wai aure ake so ayi min. Ta dafe qirji cikin zaro ido ta ce, Aure fa kika ce Asabe? Ta xaga mata kai alamar eh, Ta ce, To wa za ki aura ko dama kina da saurayi ne? Ina dashi amma ni bai yi min ba kwata-kwata. Zulfau ta ce, To ke yanzu wa kike so? Ni fa har yanzu ban samu wanda nake so ba kuma babana ya ce in fito da miji, wai in bani dashi yana da wanda zai bani, ni yanzu shawara nake so ki bani. Zulfau ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, Ni da a ganina tunda da wanda kike so kawai ki karvi zavin da mahaifinki ya yi miki. Zulfau to ai ni bansan wane ne mijin da ya zava ba. Za ki san shi ne ke da kawai ki yiwa mahaifinki biyayya. Ta ce, Kina gani haka xin ya dace? Ta xaga mata kai alamar eh! Ta ce, To shi kenan Allah ya zava mana mafi alkhairi. Zulfau ta ce, Ameen, abin da ya dace kenan ki yi addua. Alhaji Salisu zaune shi da yarsa Muhibbat suna hira, ta ce, Daddy wallahi ba kaga yadda na matsu gobe ta yi ba naga mun xau hanyar Malumfashi, rabo na da zuwa fa kusan shekara huxu kenan.” Ya ce, Haka ne Muhibbat rabonki da zuwa tun zuwan da ku ka yi, ki kaga macijin nana ki yiwa garin bore.” Ta yi dariya alamun tunowa da lokacin yadda ta ringa kurma ihu daga ganin maciji a gona. Ta ce, Dama kuwa Daddy ina da qawaye yan Malumfashi waxanda muka haxu dasu a makaranta kaga in naje sai in nemesu. Ki dai yi addua Allah ya kai mu goben muje lafiya. Ta ce, “Dady amma dai in munje zamu daxe ko danni wallahi ina son zuwa.” Ya ce, Eh mana in muka je za ki gani har sai kin gaji da zaman garin don zamu kwana biyu a can kika sani ko Allah ya baki miji don can shi kenan sai zaman can. Ta rufe fuska tana dariya ta ce, Kai Daddy ni

Leave A Reply

Your email address will not be published.