Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:8

0 0

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol

Deeja ce zaune a tsakar gida ta buga uban tagumi yau satin biyu in tayi abin sanaa ba a siya sai tai kwantai. Saboda Ahmad ya hana Zulfau talla duk abin duniya yabi yadame tarasa ya zatatayi Zilfau xin ma ta daina zaman gidan kwata kwata tana gidan shegeyar kakar Amma miqe watai ta zari mayafin ta gidan kawarta Ladoyo tafu ta tarad da ita Deeja ta ce, Lafiya Deeja da tsakar rannar nan ina fa laifiya abubuwa duk sun juyan baya komai ya lalace.Ban gane komai ya lalace bamai kika nufi Deeja. Kedai Ladiyo komai mayalala ce duk yanzu babu sanaa kimai nayi haka zan xauki kaya ko kare baya shinshi nawa. Ke Deeja bari faxar wannan mugun labarin ni yaushe rabon da niji wai asara lallai sai kin miqe tsaye to ina yar talla taki?. Ke dai “Ladiyo a tunda na kama ta nai mata mugun dukan uaban yahana yi mini talla kwata-kwata batan zaman gidan kullum tana gidan shegun kakanin nan nata marasa mutunci Jakar uba nan shine ke kuma kika kyalesu haka baki xau mataki ba bar ni da su akwai wani boka sha yanzu magani yanzu tun kafin mubar gun aiki zai faraci”, Don Allah Ladiyo da gaske kike? Qwarai ma kuwa ke dai taso mujen sa yanzu dan ba lokacion zama bane, “Ya kama ta a ce, kin miqe tsaye kinga ba yan waxan nan mutunan in kuwa baha ka ba su sunga bayan ki surabaki dagi dan tunda ke ba haihu kike ba inga kin tashi a tutar babu . Maganarki gaskiya Ladiyo ai ni duk bayi wannan tunanin ba sai shirme kwai nake tabkawa ai kuwa suna haxu da bokan a take a wajan ya cire wa Ahmadu tau syin Zulafau a ransa ya bata wani garin magani ya ce, a Tasa mai a abinci ya ci. Suna koma wa gida kuwa ta barbaxa mai cikin abinci, taka ma murana don tasan aikin ma ya ci ya gama. Dai dai wannan lokacin Zulfau ta shigo gidan tabita da wani matsiyacin kallo ta ce, Lallai yarinya kin samu sake zaki gane baki da wayo sai na yi maganin ki sai kinga ne kuranki,wai ma in tambayi ki daga gidan uba wa kike?. Makaran ta naje ba a tashi da wuri ba da a ka ta shi shi ne yabi ya gidan su Amma. Ke dan Allah yi min shiru uban wa kike ga yana zuwa makaran ta duk yaran unguwan nan in bake da shgeyar kawan nan takiba kini bibiyar yarin ya nan ba to daga yau na soke ungo tabrya in kin surfa wannan masarar ki bakace kin kai niqa. Ta ce, ki yi haquri wallahi hanuna ba lafiya kin gansu duk ciwo ne, ta nuna mata hannun fatr suk tai varo-varo kamar wadda ta qone. To wallahi a haka za ki dake ko da hannun zai karye munafuka makira. Tasa hannun ta tsinke ta da wani lafiyayan mari ji kake tas gaba xaya ta zube aqasa karara marin a kenana Ahmadu da ke xaki zaune axaki yaci abinci da Deeja tasa masa magani yayi sauri ya fito. Da gudu ta fita ta rungume Ahmad ya ce, Me ya faru wannan wane irin duka ne Deeja ta ce, tun da safe ta fita yawo sai yanzu min musa da rashin kunya. Ahmad ya ce,Ke Zulfau me ya sa za ta saki aiki ki qiyi, ciin kuka ta ce, Abu ba qin yi na yi ba kaga hanuna ciwon nan ne da kace na dai na xaukar komai zaka ta san ka sa min magani, Bana san musu tunda ta saki aiki kiyi mata, mai yasa wani lokacin ke ba kya jin magana, maza je ki daka mata. Idon ta ya cuko da hawaye ya san baza taba iya wa ba da hannun ta a haka. Ta ce, Abu wallahi bazan iya da kawa ba, ya daka mata tsawa,Maza ki xauka ki daka ko in bike ki a nan wajan. Tana dakawa hanun ta na xayewa kafin ta gama duk hannun ya kwashe ta ci kuka ta qoashi hannun sai zugi da raxaxi yake yi mata. Ba abin da ta fi so a wannan lokacin sai mutuwar ta zata fiye mata a rayuwa nan da take ciki wai dama haka kowa ya ke ji in rsa mahifiya ko ita kaxai ce tak e fuskan tar haka tagama surfen amma yaka sa baka ce wa sabo tsananin zugi da hannun ta yanke a haka dai ta xaure hannun sai zafi yake mata ta bukci ta xauka dan takai mata xaka ta ce, Deeja gashi na gama. Ta bita da kallo ta ce, Dan uban ki wakika mai da bawan ki da zan kai miki nikan inji Koni kike so na xauka nakai miki. Ta girgiza kai ta ce, Deeja kuxin niqan sai in kai ta je fama mata naira a shirin, haka ta xauka tatafi hannun sai zugi yake mata ta kai aka niqa mata. Mai makon ta dawo gida sai tayi gidan su Amma, Amma tana ganin ta tace yar Deeja daga ina kuma. Ta zunvuru baki ta ce, “Wallahi, amma zan daina zuwa gidanki idan kina ce min yar gidan Deeja,au wallaha bayar ta bacen wannan muguwar matar mara imani azzaluma. ta sauke kwanan niqan da takai ta ce, Amma jibi fa hannu na yarda ya yi, ta kama hannun ta gani ta ce, Qo newa kikai ba kije an miki addu,a ba kika barshi haka iska na shiga. Mardiyya ta fito daga xaki ta e, ba wani qonewa wahala ce kawai da Deeja ke gana mata. Amma ta ce, wannan yarinya tana shan baqar wahala, Mardiyya maza jeki kira Babanku ya zo yasa mata magani ba a son abar ciwo abuxe saboda kar wani ciwon ya shiga kita haquri Zulfau Allah na nan shi zai miki sakayya. tare suka shigo ya ce, Amma lafiya na ganki ke da kishiyar ta ki? ta ce, Malam dubi hannun yarinyar nan yanda ya yi don Allah, ya kama hannun ta ya gani cikin tausayi ya ce, qo newa kikai Zulfau? Amma ta ce, ba qonewa tayi ba kawai tsabar aikin da takene na surfe, ya girgiza kai ya shiga xakinsa ya xauko magani ya kwance vledar maganin ya fara baxa mata, ta runtse idonta; wayyo Allah Malam akwai a zafi yi haquri ke da na sanki a jarumta duk hannun ya baxe shi da ya kalleta da tausayinta ya qara kamashi ya ce, Zulfau amma kina wanka kuwa ya cire mata xan kwali ya ce, ai kanki ma duk ya yi datti ma anayi miki kitso ma kuwa? Mardiyya ta ce, Baba ina taga lokacin yin hakan ai wannan muguwar matar yaushe zata bar ta tayi wani wanka balantana wanke kai, ya ce, to abinda za ayi yanzu ke Mardiyya samata ruwa tayi wanka sannan ki wanke mata kai. Amma ta ce, ai yanzu inta zauna wani laifin zatayi gwanda taje takai mata garinta sai ta dawo, to shikenan ke Mardiyya xaura ruwa akan wuta kafin ta dawo, maza tashi ki kaima ta inba haka ba ta jibgeki. Ta zumvura baki ta xauki kwanon ta fice, cikn zolaya ya ce, amarya ta ko sallama babu kika wuce.Amma ta ce bacin ka vata mata rai shine kake so tayi ma sallama. Ya ce, wallahi tausayin Zulfau na keji duk ta gama lalacewa sai kace ba ita ba, tayi ajiyar zuciya ta ce, kai dai bari Malam ni kaina baqin cikin da nake ciki in naga Zulfau ace yarinya bata da gata agidan mahaifinta kullum cikin izaya da muguntar kishiyar uwa take tunda mahaifiyarta ta rasu ta koma baiwa a gidan kullum bata da hutu kuma kullum cikin muzguna mata ake, ya ce hka ne Amma wata rana sai labari. A tsakar gida ta sami ta a zaune ta xaura kafa xaya kan xaya sai faman girgiza kai take tana huci. Zulfau na ganin haka ta ce, Na shiga uku nasan yau sai takusa kashe ni.” “To tunkiya uwar tunvele daga gidan uban wa kike sai yanzu ki kaga da man da wowa ko, Sabo dake ballagaza ce, karya, Wallahi yau sai naga mai raba ni dake a gida, ko uban naki bai isa yahana ni dukan ki wallahi. Cikin alamun kuka ta ce, Dan Allah Deeja kiya haquri wallahi bazan sake ba. Shege ya ai a nan kifa fi auki wajan ba mutum haquri idan kika mai laifi, dalla wuce kikai min gari kicin, tun xazu nake jiran ki sai da kika gama gan tallin ki ki dawo ko. Sumui-sumui ta shiga kicin ta ajeye, tana fitowa ta ci saa Deeja ta shiga xaki ai kuwa tai sauri tafice daga gidan, gidan su Amma ta koma ta tadda har ruwan yayi zafi Amma ta ce, Taje ta juye ruwan taje tai wanka sannan a wanke mata kai xin ta juya ruwan zafin taje tayi wanka ta fito Mardiyya ta sa omo ta wanke mata kan tas sai sheqi yake tasa mata mai ta shefe mata shi ta taje wanda ya zubu mai yawa ne dan ya xan kare, ta fi wata a kitse duk da haka yana da tsawo da yake kakar ta ta biyu a gashin dan Amma a kwai gashi sosai ko da dai ta fara tsufa Amma har yanzu tana kwai ga shi. Har gadon baya fa yalwar gashin ce tai mata duk jelolin gashi sun sauko har kafa xinta. Mallam ya shi yaga yarda ya jikarsa ta koma ya ce, Koke fa Mardiyya kin fito min da amarya. Amma ta ce, sauran kuxin kitso sai ka biya. Malam ya ce, ai ko bakice ba, yanzun nan zan bayar. Yasa hannu a aljihu ya fidda naira hamsin ya ce, Mardiyya gashi ladar kitson da kika yiwa amaryata. “Aa Baba ka barshi. Bani na baki ba ki amsa mana. Tasa hannu biyu ta ce, angode. Amma ta ce to nima ai sai a bani nawa kuxin kitson ko?. Ya kwashe da dariya ya ce, kishi kike dan naba amarya ta kuxin kitso. Ta ce, ba dole nayi kishi ba wannan mai kama da larabawan tana so ta qwace min mijina, aiko bazan yarda ba nima zan fara zama yar gayu. Dukkan su suka kwashe da dariya har da Zulfau ya ce, Ai sai ki bari idan kinyi kitso sai inbiya.” Mardiyya ta ce, “Amma ina ma ni nake da wannan gashi haka.” Ya ce, ashe kishi kuke keda uwar taki amarya ta ta fiku kyau da gashi. Amma ta ce, Mardiyya tashi ki zubo mana abinci. Ta zubo musu abincin sukaci sai bayan sallar magariba Zulfau ta koma gida, a hankali ta lallava ta kwanta ba tare da an sani ba. Ana kiran sallar asuba tabar gidan ta gudo gidan su Amma, a qofar gida ta haxu da Malam. Ya ce, Zulfau ya akayi na ganki da sassafe haka Ta ce, Ba komai ina tsoron kar Deeja ta dake nine shiyasa na taho. To mushiga, suna shiga suka tadda Amma ta idar da sallah. Ta ce, Ke Zulfau daga ina haka da safiyar nan. Malam ya ce, Nima na fito daga masallaci ne zan shigo gida na haxu da ita wai ta gudo ne wai kar Deeja ta dake ta. Ta gyxa kai ba tare da ta ce qala ba, suka samu wuri suka zauna. Malam ya ce, Muga ciwon naki ya kame. Ta nuna masa. Ya ce, Yauwa ya yi kyau haka ake so kina zuwa makaranta ne. Ta ce, Eh! Amma yanzu nadai na zuwa Deeja ta hanani. Amma ta ce, Itama makarantar ta hanaki zuwa sabo da tsabar mugunta. Malam ya ce, Kinyi nisa a karatun naki, ta ce, Yanzu a sabbi nake.

KuryaNg

Leave A Reply

Your email address will not be published.