Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:7

0 3

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:7

Ya yi murmushi irin nasu na manya ya ce, “Uzairu kenan, kana nufin ba zaka iya riqe mata bane?” “Ba haka bane Dady, ni na fiso sai nan da shekara kamar uku haka.” Aa Uzairu addua zaka yi tayi Allah ya zava maka mace ta gari kuma nima ina taya ka a matsayina na mahaifin ka ina so ka auri mace ta gari na sami jikoki masu tarbiyya da nutsuwa wanda zan yi alfahari dasu. Ya ce, To Dady za a ci gaba da addua in sha Allahu.” Sannan ya ci gaba da cewa, “Matan ne yanzu ni tsoro ma suke bani wallahi. Kawai dai sai dai addu’ar kamar yadda ka ce Dady.” Dady ya gyaxa kai, “Tun da ka kammala karatunka sai ka koma kamfanin tumatir ka ci gaba da kula da shi Uzairu.” “Dady ni da aikin gwamnati zan fara.” “Wane irin aikin gwamnati Uzairu bayan Allah ya yi min arzikina dai-dai gwargwado. In kuma kamfanin tumatir xin ne bai maka ba sai ka koma na roba ko takalma.” “Haka ma ya yi duk yarda ka ce haka zaayi.” “To shike nan Allah yasa albarka a ciki.” Dab da rana zata faxi suka shiga cikin gida tsaye yasa mu Muhibbat a falo rataye da jaka ta yi kwalliya cikin wasu matsattsun riga da wando. Uzairu yabi ta da kallo,cikin vacin rai ya ce, Ke yanzu waxannan kayan zaki fita. Hajiya Mariya ta ce, faxan da nagama yi mata ke nan yanzu kuka shigo,Alha Salisu ya ce, ai keki ka sata wa yake sata inba keba laifin waye ai naki ne tun farko na nuna miki illar irin wannan shigar amma ki ke cewa yarinta ce, in ta girma zata daina yanzun data girma ba sai ki cire mata son abin a zuciyarta ba.” Ya yi vangarensa cikin vacin rai. Uzairu ya ce, “Na baki minti biyu ki nemi kayan mutunci kisa a jikin ki kafin na fito. Ya yi hanyar kicin. Ta kalli ‘yar tata, ta ce, “Kin ga dai kije ki cire kayan nan, a to don wallahi kin fini sanin halin Uzairu in ya gamu dake, kar ma ki sakoni a taimakon ki.” Ta miqe tana zunvure-zunvure a Ni gaskiya Yaya Uzairu yana takura min shi yasa bana son ya dawo.” “Ke ki ka sani in ma ba kya son ki cire dawo ki zauna, don na san dai duk girman da ki ka yi Uzairu ba zai yi shayin dukan ki ba.” Tana bubbuga qafa ta shiga xakinta ta sako wata riga da siket na atamfa ja da ratsin baqi duk da shima dai xinkin ya matseta amma ba kamar kayan baya ba. Har xakinsa ta bishi ta san halinshi sai da ta rngaxa sallama kusan sau huxu sannan ta shiga. Tana shiga ya galla mata harara da taji jikinta ya fara vari ya ce, Ban hana ki shigo min xaki kai tsaye ba.? Ta ce, Wallahi yaya Uzairu na yi sallama, ya ce da kika yi kin jiran na baki izinin shigowa ne? ta girgiza kai alama aa ya ce, To me ya kawo ki xakina.? Ta zumvura baki sannan ta ce, Yaya Uzairu naga ka dawo ko tsaraba ba ka bani ba, shine nazo na amsa. Ya galla mata harara Ya ce, lokacin da zan tafi makarantar kinban kuxin jirgi ne? ta ce, To ba Dady ya baka ba.” Tunda kuma ya bani kuxin jirgi sai ya ce mini har da na tsara ya bani ko? Maganar ta so bata dariya, amma ta gimtse kawai ba ta yi ba ta san halin yaya Uzairu. Ta ce , “Kai yaya Uzairu Da yaga dai a lamar za ta cika shi da surutu sai ya ce, Don Allah Muhibba kar ki dame ni ki bari gobe in na buxe tsarabar, sai ki karva. Yanzu ina wani uzuri ne.” Ta ce, to Yaya, ta juya zata fita ta hango Laptop ta ce, Lah! Yaya Uzairu wannan laptop xin fa mai kyau? Amma sabuwar shigowa don ban tava ganin irin design xin ba.” Ta kai hannun zata xauka yayi sauri ya buge hannun,Wai mai yasa kin fiya rawar kai ne Muhibbat,zo ki fice min daga xaki. Kai Yaya korata kake bakaga na sauya kayan da kace na sauyaba, Ya ce, ban gani ba kin san ban fiye son magana tai ya wa ba ko. Allah yaba ka haquri kaga tafiya ta baka buqatar komai na siyo maka, shopping za ni.” Cikin xaga murya ya ce, Wai ba ce wa nayi kifi cemin daga xaki ba? Idan na qaraganin qafar ki a xaki na sai na saki kuka wallahi. Tayi waje tamita shi Yaya Uzairu akwai shi da balai sai kace ni ba ‘yaruwar sa bace, yake ya mani haka a falo tasami momy a zaune ta ce, Mai kuma ya haxa ki da yayan naki, Momy kawai dan nashiga xakin sa shine yake kora ta wai kar na qara shigo masa inba haka ba sai ya sani kuka. Kyaleshi kinsan hallin yayan naki miskili ne ba ko yaushe yake son sirutu ba. Momy ni wallahi daga yau bazan sake shiga xakin shi ba. ****

Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:6

Leave A Reply

Your email address will not be published.