Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:15

0 24

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:15

taso muje ka rakani in kuma ba zaka ba ni in tafi tun kafin ta vace mana.
Ya ce, To tashi muje, suka tashi suna binta a baya har suka ga gidan da ta shiga.
Aminu ya ce, Daman na ce bazai wuce baqin gidan Malam Kabiru ba ina ga jikarsa ce don yana da babban xa a cikin birni.
Ya ce, To yanzu ya za a yi Aminu?
Ya ce, Ya kuwa za a yi ba kai ka ce kaji ka gani ba ai ga ta nan sai ka nemeta.
Ya ce, To an jima bayan sallar magariba zaka rakani.
Aminu ya yi masa wani irin kallo ya ce, Wai kai da gaske kake kenan au kana sha da wasa nake.
Ya ce, To shi kenan Allah ya kaimu anjima xin. Suka juya suka bar qofar gidan.
Lokacin da Muhibbat ta shiga gida ta tarar da Momynta da kakarta wanda suke kira Goggo.
Hajiya Mariya ta ce, Sarkin yawo har an dawo kenan.
Ta samu guri ta zauna ta ce, Wash! Momy wallahi duk na gaji.
Goggo ta ce, Ba dole ki gaji ba kina biyewa yan matan nan gwanda su sun saba ke kuma kinga baki saba ba.
Ta ce, Haba dai Goggo ai muma muna yi a garinmu sai dai ba irin wannan ba.
Hajiya Mariya ta ce, Sai ki tashi ki je ki yi wanka da sallah sannan ki ci abinci.
Ta ce, To Momy. Ta tashi ta shige xakinsu.
Goggo ta yi murmushi ta ce, Ita dai Muhibbat ba ruwanta komai ta gani ita dai ta yi wasa.
Ai ni Goggo na rasa irin Muhibbat ko gajiya bata yi da wasa ta girma amma har yanzu hankali bai zo mata ba.
Mariya kenan quruciya ce kawai ki daina damunta wata rana idan aka ce ta yi ba zata yi ba, bari dai ta yi aure har ta haihu to lokacin ne zata yi hankali.
Kayya! Goggo ni banga alamar Muhibbat zata yi hankali ba shekarunta fa sha bakwai ai ya ci ace ta yi hankali.
Ta ce, Ke kaka ga haka amma ai akwai ma waxanda suka girmeta wasu ma har yaya amma basu yi hankali ba ai ni na ga ma Muhibbat tana da hankali akan yan matan garin ga namu kiga mace har mace wata har xa ta haihu amma bata daina haukan quruciya b a.
Haka dai suka ci gaba da hirarsu har kusan magariba sannan suka tashi suka shiga ciki.
Shi kuwa abokin Aminu tun da ya koma gida ya qosa anjima ta yi don yaje ya gabatar da kansa a wajen kyakkyawar yarinyar da ya gani.
Wani vangare na zuciyarsa ta ce, To yanzu in kaje ka ce mata me kaga gani yata aminta da kai a matsayinkak na xan qauye kasan halin yan matan birni akwai su da rainin wayo.
Ya yi saurin girgiza kai ya ce, Ina wannan ita daban ce ba irin su bace shi kai yake ta karatun wasiqar jika har sai da aka kira sallah sannan ya tahsi don gabatar da farilla.
Ana idarwa ya shigo gidan yaje ya yi wanka yana fitowa ya zauna bakin katifarsa ya rasa ma wane irin kaya ya dace ya sa, sai fito da kaya yake ya rasa ma wanda zai sa a ciki daga qarshe dai ya yanke shawarar sanya wata shadda galila mai ruwan zuma wadda aka yi mata xinkin zamani an yi mata aikin sama wanda ya qara mata kyau sosai yasa ta ta yi masa matuqar kyau ya xauko takalmi shi ma dai mai ruwan zuman ne ya saka ya xauko hularsa ya saka nan da nan ya haxe a gaskiya Alyasau yana da kyau fatar jikinshi irin mai kyau ce baqa yana da idanu dara-dara wanda suka qarawa fuskarshi da kwarjini, Alyasau irin mazajen nan ne da ka kallesu za ka gane ba ragwaye bane yana da faffaxar qirji irin na jaruman maza fuskar shi xauke da saje wanda ya yi matuqar qarawa fuskarsa kyau ya xauki lafiyayyen turaren shi ya fesa jikin shi, nan da nan ya xauki qamshi mai daxi.
Ya fito daga xakin ya kulle, mahaifiyarsa ya samu zaune tana cin abinci ta bishi da kallo ta ce, Aa Alyasau ina za a kuma haka naga an sha wanka sai qamshin turare kake?
Ya sosa qeya cikin jin kunya ya ce, Dama Aminu zan raka.
Ta katseshi da cewa Ka ce dai za a je samo min suruka dai to Allah ya bada sa a Allah ya zava maka ta gari.
Ya ce, Ameen Umma ya yi sauri ya fice.
Ta yi murmushi ta ce, Alyasau kena sarkin kunya to Allah dai ya sa a yi damu don ni farin cikina ne in ka yi aure.
Ya fice daga gida ba inda ya nufa sai gidansu Aminu abokin tafiyar tasa yana isa ya taddashi zaune a qofar gidansu ya ja tsaki ya ce, Amma Aminu akwai shi da rainin hankali wai mutumin da ya ce zai rakani kenan ya samu gurinshi ya shantake.
Aminu ya yi murmushi cikin zolaya ya ce, Aa mutumin har ka iso kenan.
Ya dalla masa harara ya ce, Wallahi Aminu akwai ka da rainin hankali sai da na gaya maka ka shirya da wuri amma da yake baka xauki abun da muhimmanci ba shi ne ka samu guri ka shantake.
Ya ce, Yi haquri angon yar birni a yi min afuwa yanzun nan zna tashi na shirya mu tafi.
Ya ja tsaki ya ce, Kai fa xan rainin hankali ne kaga Malam tashi kawai ka shiga ka shirya ina nan ina jiranka.
Ya ce, An gama angon yar birni Allah ya baka yar birni.
Alyasau ya kai masa duka ya yi sauri ya kauce ya yi cikin gida da gudu yana dariya.
Sai da ya xau kusan minti goma sannan ya fito shi kuwa Alyasau duk ya qagu ya gansu a qofar gidansu Muhibbat.
Shi ma da Aminu ba laifi haxu sai dai Alyasau ya xan fishi kyau sai dai ya nuna masa hasken fata kawai.
Ya ce, Mutumin tashi muje ga ni na fito.
Ya bishi da kallo daga sama har qasa Aminu da yaga haka ya ce, Ko bai yi bane na je na canza wata shigar? Bai ce masa qala ba ya ce, Mu je, suka kama hanya ba wanda ya ce ma wani qala da Aminu yaga bashi da niyyar yi masa magana ya ce, Wai kai Alyasau in tambayeka

Leave A Reply

Your email address will not be published.