Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:14

0 13

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:14

ina sha da wani abun da za ai miki ne ni ba abu da zakai mun illa kaje ka samo min abin da zamu ci.
Zulfau ido kawai ta bi mahaifinta dashi wai shi ne ya koma haka aka maida shi sai ka ce wani sauna ji ta yi tausayin baban nata ya kamata ta fara zubar da hawaye.
To uban wa kikewa kuka wani abun aka yi miki eye ko iskancin ne nake ya motsa kinibibiya, maza tashi ki kama aiki ai baki ga hutu ba a gidan ga baida tsofaffin banzan suke xaure miki gindi kina yin abin da ki kaga dama to zan yi maganinki daga ke har su xin sai kun xanxani wahalata.
Haka ta miqe jiki ba kwari ta fara yi mata aiki ba ji ba gani in ta yi wancen ta ta kama ta gama ta sake xauko wani ta bata sai da taga ta galabaita sosai sannan ta kyaleta bata yi minti biyu ba da zama ta ce mata, Maza ta tashi ta gyara xakin da zata zauna haka ta miqe jiki ba kwari taje ta buxe xakin duk ya yi datti rabon da ta shiga xaki kusan sati uku duk ya yi dattin sai da ta qara shiga ta gani haka dole ta zage ta shiga gyara xakin ba ji ba gani sai da taga xakin ya yi mata yadda take so, don Zulfau akwai so tsabta sai dai bayar da zata yi dole ta ji tsabtarta gefe rayuwa kenan.

GARIN MALUMFASHI
S
u Uzairu an sauka garin Malumfashi lafiya yau kwanansu biyar acan duk sun zagaya yan uwa da abokan arziqi sai yau ne ya gane ashe suna da yan uwa ko da yake bazai yi mamaki ba tunda shi ba a qasar yake ba ballantana ya sansa.
Zaune yake shi da wani sabon abokin da ya yi xan Malumfashi Uzairu ya ce, Ni dai garinku xinga yana burgeni sosai kamar na yi ta zama a cikinsa.
Abokin nasa mai suna Bello ya ce, Haka garin akwai daxin zama sosai amma ga wanda ya saba da zama.
Uzairu ya ce, Kamar ya ya ga wanda ya saba da zama, kai baka jin daxin zama ne?
Haka ne kasna da wanda ya yi rayuwa a turai da wanda ya yi a qasar mu ta Nigeria daban ne.
Kai yanzu kana nufin ba anan ka yi rayuwa ba kenan?
Ya ce, Eh to zan iya ce ma haka xin ni haifaffen garin Malumfashi ne amma ba a ciki na yi rayuwa a qasar waje na yi ban tava zaman Nigeria ba na yi wata xaya kaga kuwa dole in ce nafi jin daxin can xin saboda ba zafi kaga kuwa nan in aka yi rana sai ka ji kamar fatar jikinka za ta xauke.
Uzairu ya yi murmushi ya ce, Maganarka haka take rayuwar turai akwai daxi don nina na yita don a can nake karatu ban daxe da dawowa ba muka taho wannan garin.
Ya ce, Ashe kai ma ka yi rayuwar turai kenan?
Eh na yi amma ba wani daxewa na yi ba.
Har ka gama karatun naka kenan?
Na kammala yanzun ma aiki nake so na fara yi.
Ya ce, Allah ya taimaka.
Uzairu ya amsa da Ameen.
Suna zaune suka ji an fara kiran sallar laasar dukkansu suka tashi don zuwa ba da farali.
Nasan mai karatu zai so ya ji wai ina sarkin surutu ne Muhibbat autar Hajiya Mariya yar gaban goshi bari muje mu ji ina ta shige.
Gungun yan mata ne kusan su bakwai sai wasan guje-guje suke yi na yar vuya cikin yan matan nan har da Muhibbat a ciki kana ganinta zaka gane ta fita daban a cikinsu, wani yadin material ne a jikinta wanda aka yi mata xinkin riga da siket ya yi matuqar yi mata kyau sosai Muhibbat doguwa ce tana da qiba amma ba sosai ba jikinta nata na dai dai misali fuskarta na xauke da manya-manya idanuwa farare tana da hanci xan madaidaici bakinta xan qarami amma sai xan banzan surutu a cikinsa.
Suna cikin wasan wasu samari su biyu suka zo wucewa sai kallon Muhibbat suke har suna qoqarin ya yi tuntuve suna xan gotawa suka tsaya xaya ya ce, Ya ce Gaskiya Aminu waccen yarinyar ta haxu sosai kamar ba yar nan garin ba.
Xayan wanda aka kira da Aminu ya ce, To dama ka kalli waccen yarinyar ka ce mata yar nan garin da ganin yar birni ce kuma yar masu kuxi ce ina gani motar da kaga ta shigo nan garin jiya a gidan Malam Kabiru ina gani su ne don yana da xa a can birnin.
Xayan ya ce, Amma gaskiya yarinyar ta haxu Aminu mai zai hana an jima muje gidan don ni na ji son yarinyar ya kamani.
Aminu ya yi dariya ya ce, To daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaqi wai kai me yasa ba dama kaga mace kyakkyawa duk sai ka burkicewa mutane.
Yanzu ita wannan ka sani ko an yi mata miji ba ma wannan ba kasan da waccen yarinyar ta fi qarfin ta wuce saninka, dai ka tsaya a matsayin da Allah ya ajiyeka ni da a ganina waccen yarinyar bata dace da kai ba, kawai ka yi haquri.
Ya ce, Haka ma zaka ce?
To me kake so na ce ma kai ma kasan waccen yarinyar tafi qarfinka kawai ka yi haquri mu wuce.
Ya ce, To shi kenan tunda ka ce haka amma gaskiya ina son yarinyar nan har cikin raina wallahi.
Nan ya haqura suka wuce suka bar su Muhibbat anan suna wasansu.
Bayan sun gama ta kama hanya zata koma gida tana cikin tafiya ta kusa kawai gida, su kuma suna zaune gindin wani masallaci Aminu ya ganta ya yi sauri ya zunguri abokin nasa ya ce, Mutumin ga fa mutuniyar taka nan zuwa.
Ya ce, Wace ce kuma mutuniyata?
Aminu ya ce, Kai dai kalli ka gani yana kallo sai yaga ashe wannan yarinyar ce ta xazu ya ce kai aboki don Allah tashi muje inga gidan da zata shiga don wallahi ina sonta sosai tunda na gnata xazu na ji ta a raina.
Aminu ya ce, Wai kai me yasa baka da haquri.
Ya katseshi da cewa, Don Allah in dai zaka

Leave A Reply

Your email address will not be published.