Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:13

0 17

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:13

Amma ina na gama ina cikin aiki kawai sai naga mutum a kaina kamar wanda aka jeho daga sama sai wani ciccin magani yake.
Cikin tsoro Amma ta ce, Mutum kuma wane ne?
Wane ne illah Ahmadu baban Zulfau.
Ta ce, Ahmadu fa kika ce yana ina?
Gashi can a waje a tsaye.
Amma ta miqe ta fice a tsakar gida ta sameshi a tsaye sai ka ce wani soja ta bishi da kallo ta ce, Lafiya Ahmadu kai ne da sassafe a gidan namu?
Ya murtuke fuska ya ce, Yata na zo na karva.
Cikin mamaki ta ce, Yarka fa ka ce kana da wata ya ce a nan gidan.
Cikin xaga murya ya ce, Eh! yata nake so a fito min da ita yanzu.
Ran Amma ya vaci matuqa ta ce, Ashe kana da ya anan ai ni b an sani ba sai yanzu daka sanar dani.
To tunda kin sani yanzu sai a fito min da ita tunda ba wani ya haifar min ita ba.
Ran Amma in ya yi dubu ya vaci tasan duk abin da Ahmadu yake yi ba a cikin hayyacinsa yake ba ta bishi da kallo cikin tausayawa ta girgiza kai ta juya ta koma xaki ta kira Zulfau dake uwarxaki bata san ma abin da ake yi ba ta fito ta ce, Gani Amma.
Ba tare data kalleta ba ta ce, Sanyo hijabinki ki zo muje nan take jikin Zulfau ya yi sanyi don ta tabbata ba lafiya ba ta sanyo hijabin ta suka fito a tare har wajen mahaifinta.
Amma ta ce, To gata na kawo maka ita amma ka sani duk wanda ya cuci wani Allah bazai barshi ba ballantana marainiyar Allah.
Ahmadu ni na sani duk wannan abin da kake aikatawa ba a cikin hankalinka kake yin shiba ina roqon Allah ya yaye maka wannan musibar dake tare da kai.
Ta kalli Zulfau wacce take ta zubar da hawaye ta ce, Zulfau ga mahaifinki ya zo tafiya dake amma ina roqonki duk tsanani duk wuya ki yiwa mahaifinki biyayya kar ki bijire masa, kinji Zulfau duk waxannan abubuwan da ki kaga suna faruwa dake jarrabawace Allah ke miki Zulfau ki daure har ki cinye wannan jarrabawar komai na duniya da kika gani mai wucewa ne wata rana sai labari.
Zulfau ki bi mahaifinki ki koma gida don yau ya nuna mana bamu isa da ke ba, bamu da haqqi akan ki.
Ta kama hannun Zulfau ta miqa masa ta ce, To Ahmad ga yarka nan da ka ce mu baka to ga ta nan.
Idanuwanta suka cicciko da kwalla ta yi maza ta juya ta shige xaki, shi ma duk jikinsa ya yi sanyi sai yake ganin abin da ya yi bai dace ba amma ba yadda zai yi haka yaja hannun Zulfau tana kuka suka fice daga gidan.
Amm kuwa tana shiga xaki ta fashe da kuka, Mardiyya duk ta ruxe ta ce, Amma mai ya shafeki ko ya kasheta ne dama tunda na ganshi a haka fuskarshi ba alamar annuri a fuskar na gane da wnai abu ya zo mana.
Amma ta tsagaita kukanta ta ce, Mardiyya ba abin da ya yi mata illah kawai ya ansheta daga wajenmu.
Ya ansheta kika ce Amma shi ne kuma kika barshi ya tafi da ita.
To ya zan yi Mardiyya ya nuna yana son yarsa ya fi mu iko da ita kinga kuwa ya zama dole mu bashi yarsa ko muna so ko bama so ni ba abin da yasa ni kuka illa irin wahalar da yarinyar nan zata sha don yanzu abin ya zame mata biyu tunda yanzu shi ma uban nata ya daina tausayin ta kinga kuwa sai yadda Allah ya yi da ita.
Mardiyya ta ce, Amma kar ki damu in Allah ya yarda Zulfau wahalarta ta kusa qarewa.
Kayya! Kayya! Mardiyya a da dai wahalar ta ta qare lokacin da tana nan wajenmu ba yanzu data koma gidan nan ba mai maka da gidan kurkuku ba don ni gidan kurkuku zan kirashi wallahi yadda na tsani mutuwata haka na tsani gidan Ahmadu kwata-kwata ya fice min a rai ko ta qofar gidan ban shaawar bi.
Amma yanzu abin da ya dace mu yi addua don mu nema mata sauqin wahalar da zata shiga.
Uhum! Ta yi ajiyar zuciya ta ce, Kullum cikin yinta muke Mardiyya sai dai mu qara akan na da.
Haka ne Amma Allah yasa mu dace.
Ta ce, Ameen.
Nan kowannensu ya shiga saqar zuci kowa da abin da yake saqa ba abin da yake cikin zuqatansu sai tsananin tausayin Zulfau tunda suka fice daga cikin gidansu Amma take kuka shi kuwa gogon naku ko qala bai ce mata ba abin duniya duk ya bi ya dameshi tunaninshi ya tsay haka kwakwalwarsa ta tsaya cak ya kasa tunanin komai a haka suka isa gida.
A zaune suka sameta ta bisu da wani matsiyacin kallo ta yi murmushi mai cike da mugunta, a ranta ba abin da take saqawa sai mugun abu ta ce, Matsiyata duk zan yi maganinku daga kai har yar taka.
Suka qarasa ya samu waje ya zauna ita kuma ta tsaya a tsaye sai zubar da hawaye take yi.
Ta galla mata harara ta ce, Ke don uwarki ba zaki iya zama bane kika tsayawa mutane akai.
Ta yi kamar bata san da ita take ba, ta sake qunduma mata wani ashar xin Wai ba dake nake ba shegiya, matsiyaciya wallahi in kika bari na taso sai kin gane baki da wayo.
Ya daka mata tsawa ya ce, Ba magana ake miki ba kika tsaya kina kallon mutane wai ke wata irin yarinya ce da bata ji ne wane irin kunne gareki.
Cikin sanyin jiki ta samu guri ta rakuve jikinta sai rawa yake yi ya ce, Shi kenan na cika alqawari ko? Bai qarasa ba ta yi wani irin kallo wanda sai da ya ji hanjin cikinsa ya juya ya kama bakinshi ya yi gum.
Ta ce, Sai ka tashi ka tafi ko so kake mu zauna dukkanmu mu rungume hannu, ba a bin da za mu ci.
Ya saki baki yana dariya sai ka ce wani qaramin yaro ya miqe ya ce yanzun nan zan fita

Leave A Reply

Your email address will not be published.