Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:12

0 7

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin Sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:12

Malam Musa ya kalleshi ya ce, To sarkin danne-danne aikin ka kenan kullum ko gajiya baka yi sai ka ce tare da wannan wayar aka halitto ka kullum aikin kenan Alhaji Salisu ya yi murmushi ya ce, In dai wannan abokin naka ne haka yake baida aboki hira data wuce wannan waya kullum yana tare da ita a hannunsa.
Uzairu ya ce, Kai Daddy wato zaka biyewa wannan tsohin ko don yaga bashi da ita shi ne yake ma baqin ciki.
Malam Musa ya ce, Baqin ciki mai zan yi akan wannan gwangwani abar lokacin da na yi yayin wayar tafi da gidanka ko mahaifiyarka ba a haifa ba.
Haba dai tsoho tafi da gidanka f a ka ce ai na santa ba wacce ake ajiyewa a gida ba inda ake zuwa da ita sai dai kullum tana waje xaya sai dai in an kira kazo wajen da take ka amsa.
Su dai su Hajiya Mariya kallonsu kawai suke suna wannan shirmen na jika da kaka
Muhibbat ce ta shigo hannunta riqe da waya da alamar chating take yi ko sallama bata yi ba, Uzairu ya daka mata tsawa Ke don ubanki baki iya sallama bane in dan kin zo wajen da mutane suke?
Ta turo baki ta ce, Allah Yaya na yi sallama ba dai kaji bane.
Hajiya Mariya ta ce, Aa ina kika yi sallama wato kin maida mu kurame kenan bama ji.
Malam Musa ya ce, Ni dai naji sallamar amarya lokacin da ta yi ku ne dai baku ji ba, amaryata zo nan ki zauna kusa dani ko kyale wancen mashirmacin.
Ya ce, Salisu yaushe zaku koma gidan ko zaku yi mana kwana biyu ne?
Baba zamu dai kwana xaya gobe muna so mu isa Malumfashi sai dai in mun dawo mu sake biyowa ta nan.
Ya ce, To Allah ya kaimu goben lafiya.
Dukkansu suka ce Ameen.
Bayan sun yi sallar magariba suka ci abinci aka kaisu masaukin Alhaji Salisu dashi da Uzairu aka basu falon saukar baqi.
Ita kuma Muhibbat ta ce ita a xakin matar kawunta Rabia zata kwana mai suna Jamilu.
Ita kuma Hajiya Mariya xakin mahaifiyarta ta kwanta asubar fari suka tashi kowa ya yi wanka ya yi sallah gari na wayewa suka yi sallama da kowa suka bar garin Musawa suka xau hanyar Malumfashi.
Amma ce zaune ita da Malam tana sanar dashi abin da ya faru ranshi ya yi matuqar vaci sosai ya ce, Bari zan samu shi Ahmadu xin.
Bai kamata ace ya bari ana zaluntar marainiyar Allah shi yasa tun farko naso a raba Zulfau da gidan amma ya nuna yana son yarsa zai riqeta shi yasa na kyale masa ita amma tunda abin ya zam ahaka zan je na same shi in san me ake ciki in b a zai iya riqeta bane mu ya bamu ita zamu iya riqeta har zuwa lokacin da zata sa mu miji ta yi aure.
Da dai yafi Malam don abin nata yanzu bana hankali b ane abin ya zama hauka don wata rana idan aka barta da ita a cikin gidan sai a tashi aga gawarta ta kasheta don kwata-kwata ba imani a cikin zuciyarta sai tsabar mugunta.
Ya ce, Yanzu ina Zulfaun take?
Gata can a cikin xaki a kwance.
Ya girgiza kai cikin tausayawa ya miqe ya ce, Bari naje naga jikin nata yadda ya yi.
Ta ce, To Malam.
Mardiyya ta shigo sai faman huci take da alamar an bata marai ta samu guri ta zauna.
Amma ta bita da kallo ta ce, Ke lafiyarki kuwa me ya sameki kike shigowa mutane gida rai a vace?
Ta ce, Wancen tsinanniyar matar ce ma wai kawai don na shigo gidan kiran Baban Zulfau shi ne take ta gaigaya min maganganu har da zagi ta kama yi, wai mun mallake mata miji mun hana ya kula da ita kuma wai mun rabashi da yarshi saboda tsabar mugunta, wai har da cewa babanmu yake zugashi yanayi mata wulaqanci ni kuma shi ne na dake.
Haba Mardiyya ban haki biyema na ce miki don kika ga tana haukanta ki daina biyema ki xinga kyaleta.
Amma zaginku fa take ta yi.
To data zaginmu kinga ya yi mana wani illa ne.
Malam ya fito ya ce, Lafiya na ji ku sai magana kuke yi.
Amma ta ce, Wai daga kawai na aiketa ta kira min Ahmadu ina son ganinsa shi ne taje ta biyewa Deeja sukai ta musayen yawu da ita.
Ya ce, Wai ke Mardiyya me yasa bakya ji ne ban miki magana akan rigimar nan da kike yi ba wai ke bakya ganiya ne.
Ta ce, Wallahi Baba zaginku take yi.
Ya katseta da cewa To data zagemu ke ta zaga da zaki biye mata kuna faxa ke Mardiyya bana son shashanci daga yau ma na hanaki shiga wannan gidan kina ji ko?
Ta xaga masa kai alamar taji, ya ce, Maza tashi ki ba mutane wuri.
Sumui-sumui ta tashi ta shige xaki, Amma ta ce, Malam shi ma fa Ahmadu ba haka ta barshi ba in ka duba yanzu duk baya cikin hayyacinsa ba wani abun ma idan ya yi ba zaka ce shi ne ba kwata-kwata baya jin tausayin Zulfau yanzu gaba xaya an gusar masa da hankalisa.
Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, Amma ni na daxe da fahimtar haka wani lokacin ma in dai kika ganshi a cikin gari sai ki sha wani sabon mahaukaci ne, yau dai addua ya kamata mu xinga yi masa mu roqi Allah ya yaye masa wannan musiba da yake ciki.
Ni wallahi tunda nake ban tava ganin muguwar mata mara imani ba irin Deeja a ce kai kwata-kwata a rayuwarka ta duniya baki san tausayi ba ke dai kawai ki muzgunawa wanda kike tare dashi, amma Allah na nan komai daren daxewa gaskiya zata yi halinta wallahi sai ta yi danasani a rayuwa in dai duniya ce gata nan ta isheta riga da zani har da xan kwali wanda ma ba a haifeshi ba tana jira, ke dai yanzu bar wannan maganar kawia yanzu abin da ya dace mu maida hankalinmu wajen rayuwar Zulfau da mahaifinta yanzu su ne abin tausayi.”
Haka ne Malam yanzu dai addua ya kamata mu xinga yi musu ba dare ba rana don ceto su daga hannun muguwar matar nan mara imani.
Ya ce, Allah dai yasa mu dace mu fi qarfin zuciyarmu ta amsa da ameen.
Tsaye take ta riqe qugu sai faman yarfa masa ruwan rashin mutunci take shi kuma ya zauna ya yi tagumi.
Ta ce, Ahmad da kai fa nake magana wai me kake nufi tunda wuri kasan abin da kake ciki don bazan laminta ba ita don ubanta Zulfau an gaya mata hutu tazo yi duniya, su kuma waxancan tsofaffin banza su riqeta su hanata dawowa sai ka ce iyayenta.
Ya yi saurin kallonta ya ce, Haba Deeja bai dace ki xinga zagin tsofaffin nan ba tunda ba abin da suka yi miki.
Ta katseshi da cewa Dalla rufewa mutane baki tunda sun shanyeka sun mallakeka dole ka ce haka ma ka zama wani bayinsu, to bari kaji in gaya maka tun da wuri kaje ka ce su baka yarka kana buqatarta tun da ba su suka haifar ma ita ba.
Bai zamo ace ni ce zan zama baiwa a nan gidan ba kullum ni ce aiki ko hutu bana yi sai ka ce wata inji, don haka maza-maza ka tashi ka tafi ka dawo da ita.
Ya ce, Haba Deeja ba kiga dare ya yi ba ne ki barwa gobe mana.
Gobe! Tabxijam wallahi yanzun nan nake so kaje ka taho da ita ba sai gobe ba.
Da yaga alamar bata da niyyar dainawa tsam ya miqe ya yi shimfixarshi ya kwanta.
Ta ce, Au kwanciya ma ka yi wato ka maida ni mahaukaciya ko to wallahi baka isa ba. Ta ya ye mayafin da ya lulluba dashi.
Ya tashi zaune ya ce, Wai ke don Allah Deeja bakya gajiya da wannan masifar ne to wai yanzu me kike so na yi?
So ka ke na faxa maka abin da zaka yi?
Eh! Shi nake so ki sanar dani.
Ta ce, So nake yanzun nan ba sai gobe ba kaje gidan tsofaffin can ka ce su baka yarka abin da nake so kenan ka yi min yanzu.
Haba Deeja ki duba fa ki gani yanzu qarfe nawa yanzu ina tashi naje gidan nan yanzu ai ban yi musu adalci ba Allah Deeja ki bari zuwa gobe na xaukar miki alqawari da safe zan je na taho da ita na kawo miki. Nan dai ya shiga rarrashinta har ta yarda zuwa gobe xin ba tare da ta sake yi masa magana ba ta wuce makwancinta ta kwanta shi ma ya koma nashi makwancin ya kwanta amma fa ba don ya yi barci ya dai kwanta ne kawai ba abin da ke damun sa illah tausayin Zulfau yana ganin irin muguntar da Deeja take mata amma ya kasa yin komai akai ko ya yi niyyar yin wani abu sai yaji kwata-kwata ya kasa wai shin me ke shirin faruwa ne Allah bazai kuwa tambayeshi amanar daya bashi ba kuwa ya riqe.
Yake ta yiwa kanshi tambayoyi amma ya kasa samun amsar ko da xaya ne daga ciki bai ankara ba yaji ana kiran sallar asuba ya yi mamaki wai har yaushe ya xauki tsawon wannan lokacin yana tunani, tashi har zai tayar da ita sai kuma ya fasa don yasan idan har ya tasheta to wata masifar zai janyowa kansa ya fice daga xakin yaje ya yi alwala ya tafi masallaci bayan an sallame bai yarda ya dawo gidan ba sai da gari ya waye tangaran sannan ya shigo gida, a zaune ya sameta bakin xakinta sai faman cika take tana batsewa ta yi masa wani matsiyacin kallo wanda sia da yaji gabansa ya faxi don yasan wannan kallon ba na alkhairi bane.
Cikin isa da taqama ta ce, Ina alqawarin da ka xaukar min? sai a lokacin ma ya tuna wai ya yi mata wani alqawari amma sai ya nuna kamar bai san da wani alqawari ba.
Magana fa nake maka ka yi min shiru.
Ya ce, Ina jinki.
Amma shi ne ka yi min shiru kamar ba da kai nake ba.
To ai jira nake ki sanar dani alqawarin dana xaukar miki don ni na manta.
Ta bishi da wani matsiyacin kallo ta ce, Au haka zaka ce min wai ka manta to shi kenan tunda ka manta bari ni na tuna maka alqawarin da ka xaukar min akan maganar mu ta jiya da daddare tunda safiyar ta waye ai sai aje a cika min alqawari aje gidan waxannan tsofaffin ka ce musu su baka yarka tunda ba su suka haifa ma ita ba.
Ya ce, To ai dai kin bari garin ya gama wayewa ko bai kamata ace na yi musu sammako tunda sassafe haka ba.
Au haka zaka ce ko to shi kenan, wallahi in har baka je ka tawo da ita ba yanzu to wallahi zan bar maka gidanka don bazan zama baiwarka ba.
Ta miqe a fusace ta xauko mayafin tana shirin fita ya tareta ya ce, Haba Deeja ai duk bata kaimu ga haka ba yi haquri ki koma yanzu nan zan tafi na taho miki da ita.
Ta dalla masa harara ta juya ta koma kan tabarma ta zauna sai faman huci take.
Ya ce, Na tafi sai na dawo.
Cikin xaga murya ta ce, Kar Allah yasa ka dawo in kaje can su riqeka kar su barka ka dawo.
Bai tsaya yaji abin da zata ce ba ya ficewarshi ya barta nan sai zazzaga ruwan balaI take.
(Kai jamaa Allah ya rabamu da jarababbun mata irinsu Deeja Allah kai mana katangar qarfe dasu ameen don Nabiyyir Rahma).
Yana ficewa ya xauki hanyar gidansu Amma yana tafiya yana magana sai ka ce wani zautacce a haka ya qarasa gidan ko sallama bai yiba.
Mardiyya zaune a tsakar gida tana wanke-wanke kawai sai taga mutum akanta kamar wanda aka jeho daga sama, ta miqe tsaye ta ce, Lafiya ka shigowa mutane gida ko sallama babu.
Ya tsuke fuska ba alamar annuri ya ce, Lafiyar ce ta kawo haka.
Ta ce, Ai naga alamar akwai lafiyar a gareka. Ta yi cikin xaki tabar shi nan tsaye sai wani yamutsa fuska yake sai ka ce wanda yaga kashi.
Tana shiga xaki Amma ta ce, Har kin gama aikin?

Leave A Reply

Your email address will not be published.