Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:11

0 7

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin sirrinesirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:11

***
Lokacin da su Zulfau suka koma gida ita da Asabe, ai ko Deeja ta kamata da fara dukanta ba ji ba gani sai ihu take da dai qarfinta a kawo mata xauki amma ina da yake ba kowa a gidan sai da ta yi ma dukkan da ta kasa tashi.
Duk jikinta ya yi ruxu-ruxu da shedar bulala ita kuwa xaki ta shige tabarta anan sia faman zubar hawaye take kukan ma ya qi zuwa hawaye ne kawai ke zuba a fuskarta tana kwance anan kusan minti goma amma ta kasa motsawa ta tashi jikinta duk ya yi mata tsami sai yau ta daxa tabbatar wa da Deeja bata da Imani kuma bata qaunarta lallai so take ta illatata da gasken take faxa kullum.
Salallamin da taji ana yi ta yi sauri ta juya idonta don taga wane ne.
Mardiyya ce take salati tana tafa hannu Mai zan gani haka Zulfau mai yasa meki haka ta qarasa wajenta ta lallavo ta sai zubar hawaye take kawai ta kasa cewa komai.
Ta xauketa cak ta kaita xaki ta kwantar da ita ta cire mayafin da yake jikinta ta ci xamara dashi ta fito ta shiga kicin ta wura wuta ta sa ruwa.
Duk abin da Mardiyya ke yi Deeja na kallo daga cikin xaki don ta kasa fitowa don in tasan ita ta yiwa Zulfau wannan aika-aikan to ba zata su kwasheta da daxi ba, ta in dai yanzu kika je kuka yi rigima Abu na dawowa zata qullo min wani sharrin da zata sa ya dakeni cikin vacin rai ta ce, Shi ma baban naki biye mata yake yi komai ta faxa masa dashi yake amfani kenna ni dai don Allah Inna Mardiyya ki kyaleta kawai na barta ita da Allah shi zai bi min haqqina.
Wato kin fi so a barki tai ta dukanki gaki jaka, ta koma ta zauna sai huci take yi.
Ta ce, bazan barki a cikin gidan ba abin da za a yi yanzu ki tashi ki lallava mu tafi.
Cikin kuka bazna iya ba Abu zai yi fushi dani in ya dawo bai sameni a gidan ba.
Cikin rarrashi ta ce, Ki yi haquri Zulfau ki tashi muje ba daxewa zamu yi ni da kai na zan dawo dake in baban naki ya dawo don bazan iya barinki cikin wannan halin ba.
Ta miqe jikinta sai rawa yake Mardiyya ta riqe ta, To muje ko zan xin gata maka miki kinji ko.
A haka suka fito daga xakin tana rirriqe da ita ko takalmi bata sa ba suka fice daga cikin gidan sun tadda Amma na sallah suka jirata ta idar.
Mardiyya ta shiga zayyana mata abin da ya faru da Zulfau, ta tattakura ta rafka salati.
Yanzu dama izayar da ta yi miki kenan wato dai ba zata daina dukanki ba kenan sai dai taga bayanki ni wallahi tunda nake ban tava ganin muguwar mata ba irin Deeja ace wai ba wanda zata xinga muzgunawa sai marainiyar Allah.
Mardiyya ta ce, Amma baki san wani abu ba wai shi ma Ahmadu xin yanzu ko magana bai yi in tana dukanta bai ganin laifin Deeja sai dai yaga laifin Zulfau.
Amma ta ce, Shi kenan ta gama dashi ni dama tun da na ganshi cikin yan kwanakin naga kwata-kwata bai so Zulfau tazo nan gidan na gane ba banza Deeja ta barshi amma ba komai bari Malam ya dawo duk yarda za a yi a rabata da gidan sai an yi don wallahi bazan lamunta ina ganin ana cutar marainiyar Allah ba,
Mardiyya ta ce, Tun farko sai da na ce a raba Zulfau da gidan amma aka qi to yanzu ga abin da ya haifar maganar ki gaskiya Mardiyya nima ba yanda ban yi da Malam ba amma ya ce wai abarta gidan mahaifinta kuma wallahi daga yau Zulfau ta daina zaman gidan nan.
Da dai yafi Amma kawai a rabata da gidan shi ne abin da ya dace.
Amma ta kalli Zulfau dake ta zubar hawaye ta haquri za ki Allah ya haxaki da qarfen qafa mai wuyar fita sai kiyi haquri wata rana sai labari Mardiyya maza tashi ki zubo mata abinci da alamar ko abincin qilama bata bata ba sai taga dama ta tashi ta zubo mata tuwon masara ne da miyar kuvewa xanya taji man shanu.
Ai ko kamar jira take Mardiyya ta bata ta fara ci hannu baka hannu kwarya.
Duk sai ta basu tausayi nan da nan ta cinye, Amma ta ce, A qaro miki ko kin qoshi?
Amma ta ce, Mardiyya kawo mata ruwa ta sha don naga jikin na rawa in ba wani ikon Allah ba sai ya yi mata tsami.
Sai fama da na yi mata ruwan zafi acan gidan sannan muka tawo.
To shi kenan kawo mata ruwan in tasha sai ta samu guri ta kwanta ta huta kafin malam ya dawo sai musan abin da ake ciki.
Ta kawo mata ruwan ta sha ta wanke hannu Amma ta ce, Duba cikin waccen lokar ta kusa da gado za kiga Panadol ki bata guda biyu ta sha ta xauko ta bata ta sha ta samu guri ta yi kwanciyarta.
Misalin qarfe biyu na rana suka isa garin Musawa an yi musu tarba ta mutunci cikin babban falo gidan yi musu masauki aka kewayesu da abinci kala daban-daban sai da kowannen su ya cika cikinsa da abincin dai dai lokacin aka fara kiran sallah mahaifin Hajiya Mariya ya ce su tashi suje su gabatar da sallah.
Nan suka ta da Alhaji Salisu da Uzairu dashi mahaifin Hajiya Mariya suka fice masallaci bayan sun idar da alwala suma nan Hajiya Mariya suka yi don suma su gabatar da sallah.
Bayan sun idar da sallah basu dawo cikin gidan ba suka tsaya ana ta gaggaisawa da abokan arziqi da yan uwa sai kusan magariba sannan suka dawo gida.
Suka tadda Hajiya Mariya da mahaifiyarta zaune cikin falo suna hira suma suka zauna aka ci gaba da hira.
Mahaifin Mariya ya ce, Wai ina amarya ta take ko har ta kwanta barcin gajiya ne.
Aa Abba tana ciki ita da abokiyar surutun na kasan ta inda suka haxu daman Yaya Rabiu basa jin Allah fisshemu.
Ya ce, Daman nasan halin ta tun da kuka iso naga ta yi xakin ko tsayawa mu gaisa bata yi ba sai lokacin da na ce a kirata ku ci abinci shi ne fa ta fito.
Shi dai Uzairu yana gefe ko qala bai ce musu ba sai danne-dannen wayarsa yake.

Leave A Reply

Your email address will not be published.