Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol:10

0 12

Abin sirrine - New Edition 2020 - Hausa Novel Vol

Abin sirrine – New Edition 2020 – Hausa Novel Vol

bazan yi aure acan ba nafi son zaman nan. Ya miqe zai fita. Ta ce, Daddy ina kuma zaka muna hira? Ya ce, Zan je na huta ne don bazan fita ba yau sai gobe in Allah ya kaimu. Bayan fitarsa Hajiya Mariya ta shigo ta ce, Muhibbat ke kaxai ce a cikin falon ina Daddyn naki? Momy yana cikin xaki wai zai je ya huta. Ta ce, Yau bazai fita bane. Ya ce, Wai sai gobe yau hutawa zai yi sai Allah ya kaimu gobe. Ta ce, Allah ya kaimu goben da rai da lafiya. Ta ce, Ameen. Momy ke ma zaki je Malumfashin ne? Zan je amma zan tsaye a Musawa don ina so naga Hajiyata. Momy ki bari mana in mun dawo Malumfashin sai muje Musawan Daddy ma haka ya ce. To yo ni ai bai sanar dani ba zamu biya ta Musawa ba. Qila ya manta ne Momy. Ta ce, Ni bari na shiga xaki kema ki kashe kayan kallon nan ki wuce ki kwanta sai da safe, ta ce, To Momy ta tashi ta kashe kayan kallon ta fice cikin falon ta yi xakinta. Asalin Alhaji Salisu Abdulrazak mutumin Katsina ne su huxu ne a wajen iyayensu akwai babbansu Suraj sunan shi Salisu mai bi masa Sani sannan autansu Rabiatu duk suna nan da ransu kasancewar gidan ne na yan boko tushen gidan ya bawa duk wani xa da zai tasa a gidan damar yin karatu mai zurfi. Mahaifinsu ya rasu sai mahaifiyarsu mai suna Amina dukkansu maaikata ne in ka cire sani da yake kasuwanci shi yana zaune a cikin garin Kano yayin da Surajo yake zaune a birnin Tarayya Abuja shi da iyalinsa a can yake aiki ita kuma Rabiatu tana aure a Bakori. Alhaji Salisu ya yi karatunsa a Malumfashi tun daga firamare zuwa sakandire da zai tafi Jamia sai ya samu A.B.U Zaria a can ya haxa digirinsa a shekararsa ta qarshe Allah ya haxashi da Mariya. Soyayya mai qarfi ta qullu shi da Mariya, bayan ya bar makarantar yana leqata lokaci-lokaci ya samu aiki a Kaduna daga baya kuma aka maida shi Jihar Katsina duk wannan bai sa sun rabu da Mariya ba suna tare da alqawarin in ta gama karatu zai turo don iyayenta sun san dashi. Bayan ta gama karatun Mariya ya tura danginsa aka kai kuxin sa rana sai a lokacin ya gane Mariya ita yar Musawa ce don bata tava gaya masa ba da lokaci ya zo aka yi biki da kyar kuwan na Kaduna ya yarda aka kawota Katsina wai shi ala dole sai dai ALhaji Salisu ya sayi gida a Kaduna su zauna. Mariya su biyu ne a wajen iyayenta daga ita sai Yayarta Abida wacce take aure a Bakori har yanzu iyayenta na nan da ransu. Mariya ta tare a gidanta dake cikin birnin Katsina a nan ita ma ya saman mata aiki. Bayan aurensu da shekara biyu Mariya ta samu ciki nan fa gaba xaya hankalin kowa ya dawo kan cikin Mariya. Lokacin da cikin ya isa haihuwa Allah ya bata mai sauqi bata sha wahala ba ta haifo xanta santalalle kyakkyawa fari da shi gaba xaya suka bashi lokacinsu kowa da irin kulawar da yake bashi saboda shi ya hana ta aiki tana ji tana gani akanta zauna ta kula da tarbiyyar xanta. Dole ta haqura amma a ranta ta xau aniyar komawa aikin da zarar ya yi wayo ya isa shiga makaranta zata koma bakin aikinta. Ranar sunan yaro aka sa masa suna Uzairu ya zama xan gata ta koina suna bashi kyakkyawar kulawa da tarbiyya mai kyau yana da shekara uku aka saka shi a makaranta lokacin data tuntuve Alhaji Salisu da zancen komawa aiki bata sha wahala ya amince mata ta koma. Sai da Uzairu ya kai shekaru goma sha xaya sannan Hajiya Mariya ta kuma samun wani cikin sai dai ya bata wuya sosai kamar ba zata yi kullum suna hanyar kaita asibiti har cikin ya yi girma lokacin da zata haihu sai da ta kwana ta wuni tana naquda amma bata haihu ba sai kawai aka yi ma aiki aka ciro ya mace kyakkyawa har tafi Uzairu kyau rannan sunan ta ci sunan Muhibbat. Tun da suka haifi Muhibbat Hajiya Mariya babta sake haihuwa ba. Lokacin da Uzairu ya kammala karatunsa na sakandire sai Alhaji Salisu ya tura rashin qasar Cairo don ya ci gaba da karatunsa acan ita kuma Muhibbat lokacin da ka gama karatu tana firamare sai ta tafi makarantar yan mata ta kwana dake garin Bakori. Haka rayuwa ta ci gaba cikin jin daxi Allah ya xaukaka Alhaji Salisu sosai don yanzu yana da kamfani kusan bakwai duk kuma suna aiki. Tun asuba suka gama shiryawa qarfe shida da yan mintuna an gama zuba kaya a bot Alhaji Salisu ya xauki waya ya kira Uzairu ya ce, Kai fa ake jira ko har yanzu baka gama shiryawa ba ne. Ya ce, Gani nan zuwa Daddy na gama, cikin riga da wando ya fito sun yi matuqar yi masa kyau. Gashi nan ya yi kwance luf gwanin ban shaawa ya sha gyara, ya ce, Daddy barka da asuba, Momy ina kwana. Duk suka amsa a tare cikin kulawa ALhaji Salisu ya ce, To ka gama naka shirin gaba xaya dai ko. Ya ce, Daddy na gama. To ai shi kenan. Kowa ya yi adduar fita daga gida data tafiya Muhibbat ta ce, Daddy ni har sallama na yi kawai mu tafi don ni na qagu kamar na buxe idona na ganni a Malumfashi Daddy sai qarfe nawa za muje. Uzairu ya ce, Wai Muhibbat bakya gajiya da surutu ne kinsa mutane kin damesu. Ta zumvura baki, ta yi gaba ta barshi a nan bata ci gaba da saurarar wannan vacin ran Yayanta ba shi kullum bai da abin yi sai faxa. A farfajiyar gidan suka tarar da ita kowa ya shiga motar ALhaji shi da Hajiya a baya Muhibbat ta zauna a gaba Uzairu ne direba. Maigida ya buxe musu get suka fice suka xau

Leave A Reply

Your email address will not be published.